AMANA
. _*🌒بسم الله الرحمن الرحيم🌒*_
_*Darasinmu na yau, hadisin da ke da ala'ka da Amana 09 cikin 09.*_
°
°
_*Manzon Allaah(ﷺ) yace: {BABU CIN AMANA MAFI GIRMA A WAJEN ALLAAH A RANAR AL'KIYAMA KAMAR MUTUM DA ZAI BIYA BU'KATARSA DA MATARSA, SA'ANNAN YA RIN'KA BAYYANA SIRRINTA.}*_
°
```[Sahihu Muslim;1437,Ahmad;11673,Abu Da'wud;4870,Al-Mishkāt;3190]```
==
==
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk mutumin da yake bayyana sirrin matarsa na biyan bu'katan aure zai ha'du da Allaah a Lahira a matsayin babban maci Amana, mu kiyaye jama'a. Allaahu a'alam._
~~
~~
°°°ALLAH YA BAMU IKON KIYAYE AMANA.
Comments
Post a Comment