Posts

Showing posts from January, 2023
 LABARIN NA WANNAN MAKO BUTUN HOTON AURE               Goron Safiyar Litinin Idan ka ga mummunan pre-wedding picture, irin ka ga amarya da angon na daƙuwa, ko ka ga sun rungumi juna, ko ka ga ya damƙo ƙugunta, ko an yi sumba, to alama ce da ta ke nuna cewa iyayen banza ne su ka raini ma'auratan, ko kuma ma'auratan sun bijirewa tarbiyyar da a ka ba su ne, ko kuma dama can sun saba damƙar juna tun kafin auren. Hakana in ka ga ballagazar amarya ta na ta cashewa a wajen bikinta, ko ka ga mazarin ango ya na ta botsare-botsare cikin rawa da sunan murna, to dukansu ba su da tarbiyya, ba aji, kuma su ɗin, hoto ne mai magana na irin gurɓatattun ƴaƴan da za su zazzago duniya ne. Sun cuci ƴaƴansu, kuma sun cuci al'ummar da suke shirin haifowa baragurbi! Kwata-kwata babu cinyewa a fitsara lokacin biki. Angwaye da amaren da suka haifo manyan malamai da attajirai masu dattaku, tabbas ba su yi fitsara irin wannan ba. Sun ɓoye giggiwarsu da zumuɗinsu daga idon mu...